Published
on
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Dubai, hadaddiyar D’daular larabawa, a ranar Jumaa, 13 ga Disamba, 2024, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin kaddamarwa da sanya sunan wata cibiyar adana man fetur.
An yi kiyashin kashe akalla Dala miliyan 325 wajen samar da cibiyar.
Wannan cibiyar, mallakar kamfani mai zaman kansa na Najeriya, Oriental Energy Limited, za a kaddamar da ita a ranar 14 ga Disamba, 2024.
Bayan bikin kaddamarwar a Dubai, Mataimakin Shugaban Kasar zai wuce zuwa Saudiyya inda zai yi aikin Umrah daga ranar 16 zuwa 19 ga Disamba, 2024.
A ranar 20 ga Disamba, 2024, Shettima zai gudanar da taron tattaunawa na musamman tare da shugaban bankin raya kasashen Musulmi (IsDB) a birnin Jeddah.
Tattaunawar za ta maifa da hankali kan tsarin hadin guiwa wajen daukar nauyin shirin Special Agro-Industrial Processing Zones (SAPZ Phase II) da kuma inganta gudanar da ayyukan IsDB a Najeriya, domin karfafa bunkasar tattalin arziki da aikin gona na kasar.
Ana sa ran Mataimakin Shugaban Kasar zai dawo Najeriya kafin ko a ranar 21 ga Disamba, 2024.
Gobara ta kashe ma’aurata a Kano
Shettima heads for Dubai to represent Tinubu at launch of oil facility
Shugabar Jamiyyar Conservative Kemi Badenoch ta kare maganganunta kan Najeriya
How Kogi ex-gov, Yahaya Bello used state funds to acquire properties in Dubai, Abuja – EFCC
Tinubu returns to Nigeria Sunday after China, Dubai, UK trip
Dubai princess Sheikha Mahra divorces her husband on Instagram
Dubai: $10k bank balance, N640k fee visa application requirements not from us – UAE
Copyright © Daily Post Media Ltd